Babban Limamin Masallacin Abuja Sheikh Ibrahim Makari Ya Karbi Bakuncin Baƙin Balarabe A Abuja


Daga Comr Nura Siniya 


Shararran Malamin Addinin Musulunci A Najeriya Kuma Babban Limamin Masallacin Abuja Farfesa Ibrahim Makari Ya Karɓi Bakuncin Ibrahim Hamisu Wanda Akafi Sani Da Bakin Balarabe A Gidan Shi Dake Abuja.


A cikin satin nan ne, dai idan baku manta ba Baƙin Balarabe, ya kudurci tafiya zuwa Abuja akan raƙumi domin yi ma Farfesa Ibrahim Makari barka da Shan-ruwa wanda daga bisa ni ya dakatar dashi cewa ya hawo mota ya same shi duba da matsalolin rashin tsaro da ake fama dasu a Najeriya.


A rahoton da muka samu dai Baƙin Balarabe ƙyakkawar tarba daga Sheikh Ibrahim Makari, inda ya bashi masafki tare da yi mashi rakiya zuwa babbar majalissar ƙasa.