DA DUMI-DUMINSA: Za A Sake Duba Sakamakon Zaben Gwamna A Jihar  Kano, Cewar Muhammad Garba


Daga Muhammad Kwairi Waziri


Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Talata.


Haka zalika jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta yi kira ga mambobinta da magoya bayanta da su kwantar da hankulansu su kasance masu bin doka da oda, 


Ya ce jam’iyyar za ta yi duk mai yiwuwa a cikin tanadin doka da sauran hanyoyin da aka shimfida 

domin ganin an yi adalci a lamarin.


Sanarwar ta bayyana cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da mataimakinsa da dan takarar gwamna Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da mataimakinsa sun bayyana gamsuwarsu da yadda ‘yan jam’iyyar ke gudanar da rayuwarsu kafin zabe da lokacin da kuma bayan zabe.