Ina Kira Ga Ƴan Kwankwasiyya Da Su Daina Korewa Kwankwaso Masoyansa Na Asali Irinmu, Inji Ali Artwork
Daga Abubakar Shehu Dokoki
Fitaccen ɗan wasan Barkwancin nan Ali Artwork wanda aka fi sani da Maɗagwal ya yi kira da ƴan Kwankwasiyya da su fahimci yadda siyasa take, domin burin kowanne ɗan siyasa ne ya san dabarun da zai juya maƙiyinsa ya koma masoyin sa, sannan ya ƙara da cewa sune fa masoyan Kwankwaso na asali.
Maɗagwal ya ce "duk wanda ya ga abinda kuke min a halin yanzu koda mutum yana da sha'awar ya shigo Kwankwasiyya ya bada gudummawa to tabbas zai ji tsoro, kuma hakan kawowa siyasar Kwankwaso naƙasu ne".
Rabona duk inda yake zan same shi, kuma kai da kake tunanin idan na shigo zan tare rabonka kada ka yi mamakin rabon naka a hannuna yake, bana yi wa kowa baƙin ciki, ina yi wa kowa fatan alkairi".




0 Comments